ABNA24 : Tsohon shugaban kasar ta Murtaniya yana da sabani da shugaba mai ci a yanzu Muhammad Sheikh El-Ghazouani, akan shugabanci jam’iyyar PUSD.
Hukumar da take fada laifuka masu alaka da tattalin arzikin kasar ce ta gayyaci tsohon shugaban kasar tare da tsare shi domin amsa tambayoyi.
Ana zargin tsohon shugaban kasar ne dai da yin watanda da tattalin arzikin kasar ta hanyar bayar bayar kwangila daga tsakanin 2008 zuwa 2019 da ya shugabanci kasar.
Ana tsare da tsohon shugaban kasar ne a cikin wani hamshakin gida a cikin makarantar ‘yan sanda dake birnin Nouakchot, da a nan ne shi tsohon shugaban kasar ya taba tsare Abdallah Sunusi, tsohon hukumar leken asirin kasar Libya, kafin ya karfi cin hanci na dalar Amurka miliyan 200 daga gare shi, sannan ya sake shi.
342/